da ta sauran jihohi ke bikin cika shekara daya da hawa karagar mulki daga lokacin da aka rantsar da
su a ranar 29 ga Mayun 2015, bayan kammala zabukan da suka samar da sababbin shugabannin da
wadanda suka samu komawa kujerunsu na mulki a wa’adi na biyu.
Kamar yadda zabukan na bara suka kafa tarihi a fagen siyasar kasar, haka nan gwamnati mai ci a yanzu ta zo da salo da manufofi da tsare-tsaren shugabanci bisa taken da ta yi yakin neman zabe da shi na canji.
A lokacin da gwamnatin ta hau karagar mulki, ‘Yan Nijeriya da sauran al’ummar duniya sun damu kwarai a kan turbar rugujewa da kasar ta yi dare-dare a kai a sakamakon matsalar tsaron da ya zame wa kasar karfen kafa, don haka kowa ya zuba ido don ganin dabarar da sabon rantsattsen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi amfani da ita wajen cika alkawarin magance matsalar musamman a yankin arewa-maso-gabas da ‘Yan Boko Haram suka addaba.
A cikin shekara daya da hawansa mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna wa duniya dimbin basirarsa a kan sha’anin tsaro wanda dama fagensa ne tun daga zamanin kurciya, inda ya fatattaki ‘Yan Boko Haram din daga yankunan kananan hukumomi 14 da suka mamaye a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
‘Yan Nijeriya sun yi bankwana da yawaitar tashe-tashen bama-bamai, da kai hare-haren kisan kare-dangi da mayar da garuruwa da kauyuka kufai kamar yadda aka sha wuyar haka a ‘yan shekarun da suka gabata inda dubban rayuka da dukiyoyi ta bilyoyin nairori suka salwanta.
Hatta ‘ya’yan jam’iyyun adawa na Nijeriya sun sha fitowa fili a kafafen yada labarai suna yaba wa shugaban kasan a kan kokarin da ya yi na bullo wa matsalar tsaron ta bayan gida.
A yanzu haka sojojin na Nijeriya suna fafatawar karshe a shalkwatar ‘Yan Boko Haram da ke Dajin Sambisa inda suke samun galaba a kan ‘yan kungiyar. Fara ceto wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace a makaranta manuniya ce ta gagarumar nasarar da gwamnatin ke samu a kan matsalar tsaro. Bugu da kari, gwamnatin ta sanar da daukan ‘yansanda dubu goma (10,000) aiki domin inganta sha’anin tsaron cikin gida.
Sai dai kuma, har yanzu akwai bukatar gwamnatin ta kara yin hobbasa na daukan matakan rigakafin kunno wata fitinar a kasa musamman yadda a halin yanzu wasu tsagera suka sake kunno kai a yankin Neja Delta tare da farfasa bututun mai, da kuma matsalar hare-haren wasu miyagun makiyaya da sace-sacen jama’a ana neman kudin fansa.
Muhimmin abu na biyu da ya bayyana a fili na canjin da gwamnati mai ci ta kawo a kasa shi ne batun yaki da cin hanci da rashawa.
Ba a Nijeriya ba kwai, hatta a sauran kasashen duniya Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tana samun yabo da jinjina a kan damarar da ta daura ta yaki da cin hanci da rashawa a kasar. A sakamakon haka, an bankado badakala daban-daban da suka kunshi wadakar da aka yi da kudaden gwamnati ciki har da makudan kudin da aka ware domin sayo makamai a ofishin tshohon mai bayar da shawara a kan tsaron kasa, Kanal Sambo Dasuki.
Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa musamman EFCC sun kara samun kwanjin aiki bisa sake musu mara da gwamnati ta yi. Hukumar har yanzu tana bin diddigin kudaden da aka ware na ayyuka amma jami’an gwamnatin baya suka kasafta wa kansu. Shugaban hukumar, Ibrahim Magu ya lashi kaifin takobin damko duk wanda bincikensu ya kai kansa domin makure shi ya amayo da kudaden da ya yiwa hadiyar kafinol.
Har ila yau, a wani bangare na toshe hanyoyin da ma’aikatan gwamnati ke silalewa da kudin shigar gwamnati, gwamnati mai ci ta bullo da tsarin zuba dukkan kudaden gwamnati a cikin asusu daya. Kana ta bude wani asusun da ake zuba kudaden da ake kwatowa daga mahandama wanda a ‘yan kwanakin nan shugaban kasa ya bayyana cewa kudin da ke cikin asusun ya tasamma rabin kudin kasafin kasar da ba a taba yin irin sa ba na shekarar 2016.
Sai dai ya ce ba za a taba kudin ba har sai kotu ta yi musu wankan tsarki tukuna.
Haka nan, a wani bangare na yaki da cin hancin, shugaban kasan ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin lallabarsu su maido wa da Nijeriya kudaden satar da aka jibge a bankunansu da sauran wurare.
“Muna aiki kafada da kafada da kawayenmu a sassan duniya irin su Birtaniya, Amurka, Faransa, Jamus, Chana da Hadaddiyar Daular Larabawa domin ganowa da maido da kudaden satar da aka jibge a kasashen.” In ji wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasan a kan yada labarai, Malam Garba Shehu ya taba fitarwa.
Mai magana da yawun shugaban kasan ya kuma ce yakin da Shugaba Buhari ke yi da cin hancin ya zama abin koyi ga kasashen Afirka da ma na duniya musamman bisa irin nasarorin da ake samu a dan kankanen lokaci.
Wannan kokari da shugaban kasan yake yi na daidaita al’amaura da dawo da martabat Nijeriya a idanun duniya ya bude sabon babi na kyakkyawar hulda a tsakanin Nijeriya da manyan kasashen duniya. Sabanin gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan da ta yi bakin jini a wurinsu har suka ki sayar ma ta da makai saboda zargin tauye ‘yancin Dan Adam, da rudanin da ya dabaibaye sace ‘yan matan Chibok, da mugun cin hanci da rashawa wanda har suka jawo wa ‘Yan Nijeriya mazauna ketare cin zarafi.
Gwammnatin ta kafa tubulin farfado da tattalin arzikin na cikin gida ta hanyar dakatar da bayar da canjin kudaden waje a farashin gwamnati ga wasu kayan da za mu iya sarrafawa a cikin gida irin su shinkafa, tumatir, kaji, kifi, gilasai, mangirki, da sauran su. Kana Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bullo da wasu shirye-shirye na bayar da basussuka masu sauki ga manoma domin bunkasa tattalin arziki ta hanyar noma da rage yawan dogaro da manfetur wajen samun kudaden shiga na kasar.
Har ila yau, shugaban kasan ya kaddamar da wani bashi na kimanin naira bilyan 200 ga manoman shinkafa wanda baya ga noman shinkafar, bashin ya kuma kunshi kakkafa masana’antun casar shinkafar da na dura ta a buhu domin samar da aikin yi. Sannan an dauki matakan wayar da kan ‘Yan Nijeriya a kan muhimmanci nuna kishi wajen sayen kayan da ake sarrafawa a cikin gida domin taimaka wa farfado da masana’antunmu.
Kaso mai tsokan da aka ware wa bangaren samar da ayyukan more rayuwa a cikin kasafin kudin 2016, shi ma wani bangare ne da shugaban kasan ya ce za a yi amfani da shi domin janyo hankulan masu zuba jari daga waje.
Kasafin kudin da aka yi na shekarar 2016 kimanin naira tiriliyan shida wanda shi ne irin sa na farko a tarihin kasar, ya kara fayyace alkiblar gwamnatin ta habaka tattalin arziki.
Sai dai kuma, da yake gwamnatin ta karbi mulki ne a lokacin da farashin mai ya fadi kasa warwas sannan man ne babbar hanyar samun kudin shigar gwamnatin, fatara ta karu a tsakanin talakawa, saboda rashin aikin yi da kuma toshe hanyoyin da idan an yi sata ake sammusu wani abu daga ciki. Koda yake gwamnatin ta ce komai zai sauwaka ba da jimawa ba.
Gwamnatin ta kuma dora fifiko a kan farfado da ilmi, inda ta ce ta yi shiri tsaf don gyara sha’anin ilmi tun daga matakin firamare har zuwa jami’a. Gwamnatin ta sanar da shirinta na daukan malamai wadanda suka kammala jami’o’i su koyar a makarantun firamare kimanin dubu dari biyar (500,000) da kuma ayyana yin karatu kyauta ga daliban kimiyya da fasaha da masu nazarin malanta a jimi’o’i.
Duk da namijin kokarin da gwamnatin take yi, har yanzu wasu na ganin da sauran rina a kaba, kasancewar cin hanci ya yi yawa a bangaren na ilmi, da rashin kayan karatu da rashin kwarewar malamai wadanda suke tauye yara ga samun ilmi mai inganci.
Bayan haka, wani bangare da ake ganin an samu canji a kai shi ne yadda aka dawo da bin doka a cikin aikin gwamnati, ba kamar a zamanin gwamnatin baya ba, wanda ake amfani da wa-ka-sani-wa-ya-san ka.
Wani bangare da gwamnatin ke kara samun yabo a kai shi ne yadda ta rage kudin da ake kashewa a harkokin mulki a ofisoshi da ma’aikatunta. An dakatar da alawus-alawus da ba su wajaba ba da kuma tafiye-tafiye zuwa kasashen waje wadda galibi na shakatawa ne kawai. Bugu da kari, an rage yawan ma’aikatu da ministoci domin rage bilyoyin da ake narkawa wajen daukan nauyinsu.
Daga bangaren wutar lantarki kuwa, jim kadan da hawan Shugaba Muhammadu Buhari an samu karin yawan wutar da ake bayarwa ga ‘yan kasa. Sannan shugaban kasan ya yi alkawarin kara yawan karfin wutar daga megawatt 2000 zuwa 4000 nan da karshen shekarar nan. Haka nan ya sanar da cewa nan da shekarar 2019, gwamnatin za ta samar da megawatt dubu goma (10,000).
Sai dai akwai alamun matukar gwamnatin ba ta mike tsaye ba, zai yi wahala ta iya cimma muradinta kasancewar a halin yanzu karfin wutar ya ragu daga megawatt 2000 a sakamakon farfasa bututun da ke kai wa tashoshin samar da lantarkin gas da sabbin tsagerun Neja Delta ke yi. Koda yake shugaban kasan ya gargadi tsegerun, ko su daina ko kuma su dandana kudarsu. Inda a makon da ya wuce manyan hafsoshin sojojin kasar suka yi taro a Fatakwal, Babban Birnin Jihar Ribas domin nazarin yadda za yi maganin masu kunnen kashi.
A yayin da gwamnatin ke dab da cika shekara daya a kan karagar mulki, ta sake yin wani abu da za a iya cewa gwamnatocin baya sun kasa dangane da abin da ya shafi cire tallafin mai. A sakamakon kiki-kikar da aka yi ta yi a tsakanin gwamnatin da dillan mai masu zaman kansu kan yadda za a wadata kasar da mai, daga bisani a farkon watannan gwamnatin ta sanar da kara kudin mai daga naira tamanin da shida da kwabo biyar zuwa naira 145.
Duk da yake an dan so a kai ruwa-rana a tsakanin gwamnatin da kungiyoyin kwadago, da alama za a daidaita a kan lamarin musamman yadda kungiyoyin suka sanar da janye yajin aikin da suka fara a farkon makon nan. Babu mamaki kungiyoyin sun ga uwar bari ce, saboda ganin yadda ‘Yan Nijeriya ba su goyi bayansu ba da kuma rarrabuwar kai da aka samu a tsakanin shugabannin kwadagon.
Amma kuma kara kudin man ya haifar da tashin gwauron zabin kayayyaki, kusan komai a kasar ya kara kudi, da abin da ya shafi mai da wanda bai shafa ba, baki daya sun yi tsada. Lamarin ya sa hatta wasu da ke goyon bayan gwamnatin sun nuna matsuwa a kan wahalar da talakawa ke sha, kana suka bukaci gwamnatin ta sake bitar karin da nufin ragewa.
Daga cikin wa’adin da gwamnatin za ta yi a kan karagar mulki na tsawon shekara hudu, a halin yanzu ta ci shekara daya, yanzu ‘Yan Nijeriya za su zuba ido su ga yadda za ta kaya a lokacin da wa’adin ya raba rabi a badi idan Allah ya kai mu, musamman ma da a yanzu jam’iyyar adawa ta PDP ke kurarin cewa dole ta canja canjin da aka yi.
A halin da ake ciki kuma, CNN Hausa ta leka sassan jihohi domin nazarin canjin da suka samar wa al’ummarsu.
0 Response to "Shekara Daya Na Gwamnatin Canji: Wane Nasara Aka Samu? Car Insurance"
Post a Comment