A karon farko tun lokacin da aka fara yaki da kungiyar Boko Haram, kasar Amurka ta amince cewa zata sayarwa da Najeriya makaman yaki da kayan tattara bayanan sirri.
Rahotanni na cewa gwamnatin Amurka da yan majalisarta sun amince da irin jagorancin da shugaba Mohammadu Buhari ya keyi a yanzu, da kuma irin matakan da yake dauka don tabbatar da anbi ko’idoji na yin yaki da daukan matakan da suka zama wajibi a kasar na wanke matsalolin da aikin soja ya fuskanta ta fuskar cin hanci da rashawa da kuma lalaci wajen gudanar da ayyuka na yaki da ta’addanci musamman kungiyar Boko Haram.
Gwamnatin Najeriya ta dade tana kuka cewar bata samu hadin kai na samun makamai daga Amurka ba, abinda ake ganin ya kawo cikas da kuma jinkiri wajen nasarorin da yakamata a samu tun farko wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Matsalolin da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta fuskanta wajen yaki da Boko Haram da kuma rashin amincewar da kasashen duniya suka yiwa Najeriya, yasa Amurka ta janye jikinta da kuma bayanan sirri da take bayarwa.
0 Response to "Boko Haram Tazo Karshe. Kalli Irin Taimakon Da America Zata Ma Nijeriya."
Post a Comment