Dalilin Da Yasa Na Yankewa Dan Kishiyata Azzakari-- Inji Bara'atu Muhammad

Bara'atu Muhammad wadda ta yankewa dan kishiyata azzakari a kauyen Dafe dake jihar Niger, ta bayyana dalilinta na yin wannan mummuna aiki ga dan kishiryarta. Bara'atu dai mai shekara 17, mata ta biyu ce wajan mijinta Muhammad dauda kuma an aureta ne wata 4 da ya wuce.

Ba tare da wani tashin hankali ba dai ko kuma nuna nadama ta bayyana cewa tabbas itace ta aikata wannan mummunan aiki. Ta bayyana cewa mahaifiyar yaron tana bacci yayin da ta dauke shi ta shiga dashi bandaki ta yanke masa azzakarin nashi. Yaran dai watanshi 23 kacal a duniya.

Ta bayyana cewa dalilinta nayin wannan mummunan aiki shine domin na rama zagin da mahaifiyarsa take min kullum. Ta ce dai mahaifiyar yaron tana zaginta kullum kuma ta gayawa mijin nasa amma yaki daukar wani mataki.

Likitan da ke kula da yaron dai ya bayyana cewa ba yadda za'ayi yaron ya samu dawowar azzakarin nashi saboda haka bazai iya mu'amalar aure ko ya girma ba.


0 Response to "Dalilin Da Yasa Na Yankewa Dan Kishiyata Azzakari-- Inji Bara'atu Muhammad"

Post a Comment