Wani mai magana da yawun iyayen
matan Chibok da aka sace, Yakubu Nkeki, ya shaida wa BBC cewa ba 'yar su
sojojin Najeriya suka ceto ranar Alhamis ba.
A cewarsa, "Mun
bincika sunaye da hotunan yaran da aka sace, sannan mun tuntubi dukkan
mutanen da aka sace musu 'ya'ya, amma sun tabbatar mana cewa yarinyar ba
'yar su ba ce. Bayanan da muke da su sun tabbatar mana cewa yarinyar da
aka gano ranar Alhamis 'yar wani Fasto ce aka sace ta daga Madagali a
jihar Adamawa.".Sai dai da muka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka, wanda shi ne ya fitar da sanarwar ceto yarinyar ta biyu, ya jaddada cewa yarinyar da dakarunsu suka ceto 'yar Chibok ce.
Tun da fari dai rundunar sojan Nigeria ta ce dakarunta sun kai samame inda suka ceto yarinyar da kuma wasu mata.
Sanarwa ta ce yarinyar ta gaya musu cewa a lokacin da 'yan Boko Haram suka sace su, tana matakin ƙaramar sakandire na JSS na ɗaya.
Yarinyar ta fito ne daga garin Madagali na jihar Adamawa.
Ita ce, ta 157 a jerin sunayen 'yan matan Chibok 219 da 'yan Boko Haram suka sace cikin watan Aprilun shekara ta 2014.
Wadda aka ceto din ta kuma fadawa sojoji cewa, wasu 'yan uwanta da aka sace su tare su uku sun kuɓuce bayan sojoji sun kai sama a Shettima Aboh a ƙaramar hukumar Damboa.
Yayin samamen sojojin sun kuma ce sun ceto mata da yara ƙanana 97 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su.
Koda ranar Alhamis shugaba Muhammadu Buhari ya gana da wata daga cikin 'yan matan Chibok da aka ceto ranar Talata.
0 Response to "Ba 'yar mu aka gano ba - Iyayen matan Chibok"
Post a Comment