El-rufa'i Matsoraci Ne Kuma Gawurtaccen Mashayin Giya ne- Inji Senator Shehu Sani

Sanatan nan dai na Kaduna ta tsakiya jiya ya zo wa gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-rufai da kalamai masu zafi inda ya bayyana gwamnan a matsayin matsoraci kuma gawurtaccen dan giya.

Senator Shehu sani dai yayima gwamnan wannan mummunan zagin saboda a cewar sa gwamnan yana bayan yunkurin da jamiyyar APC reshen jihar Kaduna takeyi na korar sa daga jamiyyar na tsahon wani lokaci. A cewar senator in dai tsoro ne yasa Gwamnan ya kasa tunkararsa da takardar korar inda ya aiko kwamishinan kananan hukomimi na jihar.

Ya kuma bayyana cewa Malam Nasiru El-rufai ba masoyin shugaban kasa Buhari ne na halak ba inda ya kara da cewa shi El-rufai yanayin ladabi ga du wanda ya gani da milki ko dukiya a hannunsa. Ya kara da cewa dai Elrufai ya yi ma jamiyyar kisan gillar a jahar inda jama'a da yawa suke barin jamiyyar yanzu.

 Me zaku ce game da wannan batu?

0 Response to "El-rufa'i Matsoraci Ne Kuma Gawurtaccen Mashayin Giya ne- Inji Senator Shehu Sani"

Post a Comment