Za A Iya Samun Boko Haram Na Biyu Da Ba A Dakatar Da Zakzaky Ba, Inji Dan Uwan Zakzaky

Yayan Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky, Malam Sani Yakubu, ya bayyana cewa kungiyar shi’a a Nijeriya kungiya ce da wajibi gwamnati ta binciki al’amuranta.
Malam Sani Yakubu ya fadi haka ne yayin wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust, inda ya ce Sheikh Zakzaky dan uwan shi ne na jini sun jima suna tare tun suna kanana. “mun taso tare da Zakzaky kuma tun lokacin da ya fara bin wannan akida na Shi’a muka rabu. Kafin mu rabu sai da muka yi iya kokarin mu wajen fahimtar da shi illar abunda yake kokarin shiga.
“Ni da babban yayanmu mun yi iya kokarin mu wajen nuna masa gaskiya amma a wancan lokacin ya ce ba Shi’a yake bi ba. Kawai yana bin kungiyoyi masu yada addini ne. Ya yi ta rubuta wasiku a farkon farawar shi ga kasashen Iran da kasar Chana a shekarar 1979. A wancan lokaci, Iran ta zo ta soma aiko masa da takaddu wanda da sannu suka rinjaye shi zuwa Shi’a.
“Abunda ya faru da su kadan ne daga sakamakon zunuban su da fito-na-fito da suke yi da Allah. Sun kasance ba sa girmama hukuma ko da kuwa hukumar na ‘yan sanda, soji, jami’an tsaro da Malaman Musulunci. Ba sa sauraron kowa sai shugabannin su na Shi’a. Abunda ya faru da su a Zariya aya ce Allah ya nuna musu. Duk wani musulmi da ya ji zafin abunda ya auku da su munafiki ne.” Inji shi Malam Sani Yakubu.
Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky ya kasance a hannun jami’an tsaro tun bayan faruwan lamarin na Zariya, inda aka samu asarar rayuka da dama. Ko a baya bayan nan, kungiyar ta shi’a ta kai karar gwamnatin Nijerya da wasu shugabanni a arewa gaban majalisar dinkin duniya, inda take kalubalantar su da yi wa membobinta kisan kiyashi.

0 Response to "Za A Iya Samun Boko Haram Na Biyu Da Ba A Dakatar Da Zakzaky Ba, Inji Dan Uwan Zakzaky"

Post a Comment