BUHARI NA GANAWA YAU DA MAJALISA KAN KASAFIN KUDI

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki zai jagoranci tawagar sanatoci domin ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari a wannan Talata da nufin warware takardamar da ake samu kan kasafin kudin bana.
Tun a ranar Jummu’ar da ta gabata aka shirya wannan ganawar amma aka dage ta zuwa yau saboda wani dalili.
Ana ganin yin wannan zaman da shugaba Buhari ya zama tilas domin kuwa hakan ne zai kawo karshen rashin fahimtar juna tsakanin bangaren majalisar dokoki da na zantarwa akan kasafin kudin na bana.
Fadar shugaban kasar ta bayyana damuwarta kan yadda majalisar ta sauya wasu alkaluma a kasafin kudin, abinda ya sa Buhari ya ki sanya hannu a kai.
'Yan Najeriya dai sun kagu su ga an fara aiwatar da kasafin.

0 Response to "BUHARI NA GANAWA YAU DA MAJALISA KAN KASAFIN KUDI"

Post a Comment