Wannan na dauke ne a ckin wata sanarwa da hukumar nan dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagwon kasa EFCC ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Wilson Uwujaren.
Sanarwar ta bayyana cewa hukumar EFCC ta sami nasarar samun wani tsohon
dan majalisar dokokin jihar Kogi kuma tsohon Shugaban riko na karamar
hukumar Ogori/Magongo na jihar Gabriel Daudu da laifin zambar kudi naira
biliyan 1.4
A watan Afrilun shekarar 2010 ne hukumar EFCC ta soma gurfanar da Daudu kan zarge zarge 208, da suka danganci halartar kudaden haram da kuma barnatar da kudaden al'umma.
Mai shari'ah Inyang Ekwo wanda ya jagoranci shari'ar a wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Lokoja a jihar Kogi, ya same shi da aikata laifuka 77, sannan aka yanke masu hukuncin daurin shekaru 154 a gidan yari.
Kafin a yanke masa hukuncin mai gabatar da kara Wahab Shittu ya gabatarwa da kotun shaidu guda 13 da za su tabbatar da tuhumar da ake masa

0 Response to "An Yanke Wa Wani Tsohon Dan Majalisar Jihar Kogi Hukuncin Daurin Shekaru 154 A Gidan Wakafi"
Post a Comment