FARIN JININ BUHARI YA RAGU DA KASO 60 CIKIN 100.

Binciken da wani kamfanin dillacin labarai na IGBERE ya gudanar ya gano cewar farin jinin shugaban kasar nan Muhammadu Buhari ya fadi wan war a wurin yan Najeriya da kaso 60 cikin 100.

Hakan kuma ya biyo bayan jin ra'ayin jama'a da kamfanin ya gudanar daga ranar 1 zuwa 22 na watan Aprilun da muke ciki.

Inji kamfanin,hakan bai rasa nasaba da jin jikin da akeyi a halin yanzu,yayin da shi kuma shugaban kasar keta bidirin gaban sa.

Kamfanin na IGBERE yace ba lallai bane shugaban ya iya komawa matsayin sa a zabe mai zuwa matukar aka cigaba da yiwa yan kasa mulkin dan wanzan.

Ko kun yarda da wannan bincike ?

0 Response to "FARIN JININ BUHARI YA RAGU DA KASO 60 CIKIN 100."

Post a Comment