A karshe Tsohon Shugaban Hukumar Kwastan ta Kasa, Dikko Inde ya mika kansa ga hukumar EFCC bayan watanni shida da aka kwashe ana farautarsa.
Ana dai tuhumar Inde ne da almundahanar Naira bilyan 42 na kudaden hukumar Kwastan wadanda ya yi rub da ciki da su a lokacin yana shugaban hukumar.
CLICKIN HOTON KASA DON KOYON YADDA ZAKA GAMSAR DA IYALINKA SOSAI
A jiya Alhamis ne ya isa ofishin hukumar ta EFCC da misalin karefe goma
na safe inda aka kwashe kusan awonni takwas ana yi masa tambayoyi inda
kuma aka rike shi a hukumar da nufin ci gaba da yi masa tambayoyi a yau
Juma'a.
Idan ba a manta ba, tun a ranar 8 ga watan Janairu ne, hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman tsohon shugaban Kwastan din bayan ya arce zuwa wata kasa wanda har sai da EFCC ta nemi taimakon rundunar 'yan sanda ta kasa da kasa wato INTERPOL kan ta taimaka mata wajen farauto shi.

CLICK BELOW TO WATCH PICTURES
0 Response to "Hukumar EFCC Ta Damke Dikko Inde, Tsohon Shugaban Custom."
Post a Comment