A jihar gombe wasu ‘yan fashi da makami sun hallaka wata mata ‘yar
kasuwa ‘yar kasar kamaru sa’an nan suka kuma harbe wani malamin jami'ar
garin kashere dake jihar gomben a lokacin dasuke tafiya a cikin motoci a
kan hanyar gombe zuwa yola.
A cewar mai Magana da yawun jami’an ‘yan sandan jahar DSP Ahmed
Usman, matar mai suna Zainab Mamuda ‘yar kasuwa ce kuma ta fito sayayya
ne daga Kano akan hanyarta ta komawa kasar su sai ‘yan fashin suka tare
motar da take ciki wadda ta rasa ranta a sanadiyyar harbin da suka yi.Wani mutum da shima ya rasa ransa a cewar kakakin hukumar ‘yan sandan shine wani malamin jami’a mai suna Umar wanda suka hallaka kuma suka kwashe wayoyinsa na hannu.
Click Below to Watch The Hot Video
A wata sabuwa kuma hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu Fulani dake aikawa jama’a rubutaccen sako mai barazanar kisa idan ba’a biya masu bukatar sub a kamar yadda DSP Ahmed ya bayyana.
Ya ce “da taimakon sanannen maharbin nan Ali Kwara, mun yi nasarar cafke wasu matasa su uku wadanda suka kitsa wani yunkuri domin sace mahaifin su inda suka rubuta masa wasika ba tare da yasan cewar ‘ya’yan sa ne suka rubuta ba suka bukaci ya basu kudi Naira miliyan guda ko kuma su hallaka shi.
0 Response to "GOMBE: Ali Kwara Da 'Yan Sanda Sun Cafke Wasu Barayi "
Post a Comment