Hotunan Mutanan da aka kashe a zaben Rivers

Hukumar zabe ta kasa a Najeriya INEC, ta dakatar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisun dokoki Jiha da Tarayya da ake gudanarwa a wasu kanana hukumomin Jihar Ribas.
A cewar kakakin Hukumar Nck Dazang dakatar da zabe a kananan hukumomin Bonny, Andoni da Gokana da Khan ya biyo bayan tashin hankali da aka samu a wasu mazabun
Mista Nick ya kuma bayyana yadda a wasu mazabun aka fito da takarda sakamakon zabe na boge.
Daga daren jiya dai zuwa waye garin yau Assabar an ta harbe-harben bindiga a karamar hukumar Bonny da Elemi.

0 Response to "Hotunan Mutanan da aka kashe a zaben Rivers"

Post a Comment