'Yar Chibok ta gana da shugaba Buhari

Amina Ali Nkeki, 'yar makarantar Chibok din nan da aka ceto daga hannun Boko Haram ta isa fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Ta isa fadar ne tare da rakiyar gwamnan jihar Borno da wasu manyan jami'an gwamnati.
Ta rufe fuskarta da kyalle ta yadda babu wanda zai iya gani.
A ranar Laraba ne dai aka ceto Amina Ali da jaririyarta daga MBalala da ke kusa da garin Chibok.
Wata majiya ta shaida mana cewa an duba lafiyar Amina Ali da jaririnta a asibiti.
Wannan dai shi ne karon farko cikin shekara biyu da aka yi nasarar kuɓuto wata daga cikin 'yan matan Chibok fiye da ɗari biyu da 'yan Boko Haram suka sace.
Tun da farko dai rundunar sojan Nigeria ta ce ta miƙa yarinyar da jaririyarta ga gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.
Sojojin sun ce sun kama mutumin da aka ce shi ne mijin yarinyar ta Chibok da aka ceto.
Ɗaya daga cikin dattawan yankin Chibok ya ce, yarinyar da aka ceto ta sanar da su cewa, dukkan sauran 'yan matan suna hannun 'yan Boko Haram a dajin Sambisa.

0 Response to " 'Yar Chibok ta gana da shugaba Buhari"

Post a Comment