Rigimar Shi'a Da Saudiya:'Yan Iran ba za su je Hajjin bana ba

Ministan al'adun kasar Iran ya ce ba za su tura 'yan kasarsu aikin Hajji a wannan shekarar ba.
Ali Jannat ya ce ba zai yiwuwu 'yan Iran su yi aikin Hajjin ba, yana mai zargin Saudiyya da yin kafar-ungulu ga 'yan Iran da ke so su yi aikin Hajjin.
        Sami Kyautar Sabuwar Waya Daga BBC ta hanyar clicking Link/rubutun da ke kasa
A lokacin Hajjin bara ne dai daruruwan mahajjata suka rasa rayukansu kuma akasarinsu 'yan Iran ne a turmutsitsin da aka samu wanda kasar Iran din ta dora alhakin hakan kan hukumomin Saudiya.
Ana ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen guda biyu, a yayin da kasashen ke marawa yankunan da ke yaki daban-daban baya, cikinsu har da Syria da Yemen.
         Domin shiga sabon Whatsapp Group Inmu Na Ahlan Ya Ramadan yi Clicking Hoton Kasa

0 Response to "Rigimar Shi'a Da Saudiya:'Yan Iran ba za su je Hajjin bana ba"

Post a Comment