Taron PDP a Jigawa ya Tsorata APC.

Yadda Garin Dutse Ya Zama Babu Masaka Tsinke
A kokarin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP take don ganin ta kwace mulki a zaben 2019, a yayin ziyarar da shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Ali Modu Sheriff ya kawo garin Dutse babban birnin jihar Jigawa, ya samun kyakkyawar tarba daga wurin magoya bayan jam'iyyar dake jihar a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Alhaji Sule Lamido.
Taron, wanda aka gudanar da shi a hedikwatar jam'iyyar dake garin Dutse, ya samu halartar wasu daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar dake ciki da wajen jihar.
Wasu daga cikin manyan jam'iyyar da suka halarci taron sun hada da, shugaban jam'iyyar ta PDP, Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero (Dallatun Zazzau), tsohon ministan Abuja, Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi), tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da sauransu da dama.
Bincike ya nuna cewa dandazon magoya bayan jam'iyyar sun rako Modu Sherif tun daga filin saukar jirage har zuwa hedikwatar jam'iyyar, inda suke yi Sule Lamido kirari iri-iri.
Tuni da Modu Sheriff da sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka halarci taron suka bayyana dandazon magoya bayan jam'iyyar da suka fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar taron, a matsayin wata alama ta dawo da martabar jam'iyyar a zaben 2019.

0 Response to "Taron PDP a Jigawa ya Tsorata APC."

Post a Comment