An kashe matar da ta yi 'ɓatanci' ga Annabi a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama mutum daya, bayan kashe wata mata da aka zarga da yin ɓatanci ga Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Kano, Magaji Musa Majiya, ya shaida wa BBC cewa mutanen sun kashe matar ne, kana suka yi yunkurin kashe mijinta a kasuwar Kofar Wambai da ke birnin na Kano.
Click Below to Watch The Hot Video
A cewarsa, jami'an tsaro sun ceci mijin, kuma yanzu haka yana hannunsu, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
Rahotanni dai sun ce harkoki sun ci gaba da tafiya kamar yadda ya kamata bayan faruwar lamarin.
Sai dai an jibge jami'an tsaro a wurare da dama na birnin na Kano, musamman masallatan juma'a.

0 Response to "An kashe matar da ta yi 'ɓatanci' ga Annabi a Kano"

Post a Comment