MATASA MU YI HATTARA...!!


Na wayi gari da tunanin yadda Jahilci da ilimi ke canja rayuwar
dan-adam.
*Jahilci babu komai acikinsa sai duhu da bata. Jahilci yana canja
rayuwar dan'adam daga kyakykyawa zuwa mummuna ko kuma
daga mummuna zuwa mafi muni.
Sau da yawa zaka ga matashi ya kai matashi ga shiga ta kamala
amma maganar bakinsa kadai ta isa tabbatar maka cewa jahilci
yayi tasiri akansa.Jahilci na kawar da tunanin dan'adam daga
daidai izuwa bata.
*Ilimi tare da amfani dashi ta hanyar da ta dace na gyara
rayuwar dan'adam,daga bata izuwa daidai...
Dan'adam yakan shiga matsala amma ta hanyar yin amfani da
iliminsa sai nan da nan ya fita acikin matsala.
A addinance ko in ce a musulunci wajibine ga kowannenmu ya
nema ilimi,komai wuya komai wahala...addini baya yuwuwa saida
ilimi,shin baka karanta bane fadin Allah Madaukaki acikin
Alqur'ani Megirma "SHIN WADANDA SUKA SANI DA
WADANDA BASU SANIBA ZASU DAIDAITA". Annabi s.a.w
ya horemu da neman ilimi koda kuwa a birnin Sin ne. (watau
saboda nisa).
A zamanin nan da muka tsinci kanmu a ciki,ba ilimin addini
ba,harma da na boko ya wajaba agaremu. Saidai dan'uwana
matashi me neman ilimin boko,ka kiyaye ka kuma yi hattara,Ilimin
zamani ko in ce ilimin boko ba haramun bane a musulunce,amma
wajibin mune mu nemeshi ta hanyar da ta dace.Wajibin mu ne
muyi amfani dashi ta hanyar da ta dace.... Na lura na kuma
fahimci akwai tsaruka da suka ci karo da addinin musulunci a
makarantunmu na boko.
A shekarar karatuna ta farko a Jami'a an koyar damu ilimin
"SAMUWAR DAN'ADAM" (a tsari irin na boko) acikin abunda
akeso mu koya mu kuma sani 'dan'adam' ba halittarsa
akayiba..faruwar wasu al'amurane suka sabbaba samuwarsa.
A shekarar karatuna ta biyu na kara tabbatarwa da kaina cewa
akwai manyan matsaloli a irin tsarin karatun makarantunmu na
boko.Cakuda maza da mata a wuri daya ba matsala bace a
wajen wasu hukumomin makarantunmu na boko,to amma ai
dan'uwana matashi kasan matsalace ga kanka da kuma
addininka,don haka kayi hattara....
Na wayi gari da tunanin yadda ilimi ke canja rayuwar dan'adam
ne sakamakon wata lakca da na halarta jiya da yamma.
Acikin lakcar malamin yana kore samuwar Allah.
Subhanallah !!....yana kafa hujjojin da ko kankanin yaroma bazai
daukaba...Don Haka 'Yan'uwana matasa muyi hattara.
Allah Ka Tsaremu Ka tsare Mana Imaninmu,Ka Bamu Ilimi Me
Amfani,Me Amfanarwa Duniyarmu Da Lahirarmu.

0 Response to "MATASA MU YI HATTARA...!!"

Post a Comment