Satar Abacha:Switzerland Zata dawo Da miliyoyi

Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da aniyar da Switzerland ta nuna na dawo da dala miliyan 321 da tsohon shugaban kasar mai rasuwa Sani Abacha ya wawure.
A yanzu haka gwamnatin Najeriya na kokarin samar da wani tsari da zai taimaka wajen ganin an dawo da dukkan kudaden kasar da aka sace a can baya aka boye su a kasashen waje.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin da yake wata ganawa da wata tawaga ta kasar Switzerland a Abuja.
Farfesa Osinbajo ya ce, "Za mu tabbatar da cewa an yi amfani da dukkan kudaden da aka kwato yadda ya kamata."
Ya kuma kara da cewa da zarar an kammala samar da wannan tsari na dawo da kudaden, za a sanar da al'ummar kasa.
Daga bisani ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin kasar da ta Switzerland don batun dawo da kudaden.
Tun a shekarar 1999, aka soma batun kudaden da ake zargin Janar Abacha ya sace inda kuma kawo yanzu hukumomi a Switzerland suka taimaka aka mayar wa gwamnatin Nigeria kusan dala biliyan biyu da miliya dubu dari biyu.

0 Response to "Satar Abacha:Switzerland Zata dawo Da miliyoyi"

Post a Comment